Cire Tallafin Mai: Gwamnan Taraba Ya Ayyana Ilimi Kyauta A Makarantu
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ayyana karatun firamare da sakandare a matsayin kyauta a jihar.
Kefas ya bayyana haka ne a makarantar firamare ta Ebenezer da ke Wukari a ranar Juma’a.
A cewarsa, daga zangon karatu na gaba, za gudanar da karatu kyauta a makarantun firamare da sakandare a jihar Taraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnan Sokoto Ya Garkame Wa Ma’aikatan Gidan Gwamnati Kofa
Gwamnan ya jaddada cewa hakkin gwamnati ne ta dauki nauyin kashe kudade don haka bai kamata a rika biyan dalibai ko sisi ba.
Ya ce baya ga cika alkawarin yakin neman zabe, wahalhalun da aka samu na cire tallafin man fetur ya sa daukar matakin ya zama wajibi.
A baya dai gwamnan ya rage kudaden shiga jami’o’i da kashi 50 cikin 100 domin rage wahalhalun da yan jihar ke fuskanta a halin yanzu.
A wani labarin kuma:Gwamnan Zamfara Ya Rage Yawan Ma’aikatu Daga 28 Zuwa 16
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wata doka da za ta sake fasalin ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16.
A cewar Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan, wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, matakin shine don rage barna a cikin gwamnati tare da kawar da wasu ayyuka.