Ma’aikatar lafiya ta jihar Bayelsa ta tabbatar da bullar cutar kyandar biri a jihar, inda ta ce kawo yanzu kimanin mutane 13 ne suka kamu da cutar.
Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dr Jones Stow, ya bayyana cewa cutar ta fi kama maza fiye da mata.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Yanke Wa Ɗan Dambe Hukuncin Rataya Kan kashe Matar sa
Stow ya bayyana cewa cutar kyandar biri a matsayin cuta ta dabbobi cuta ce idan ana kamuwa da ita daga kayayyakin dabbobi ko gurbacewar yanayi ga mutane, yana haifar da rabe-raben fata da ke tasowa zuwa manyan ƙuraje musamman a yankin fuska, wanda ke haifar da tabo.
Ya kuma bayyana cewa, a lokacin da cutar ta bulla a kasar, matakan kariya sun hada da; kula da abinci daidai lokacin dafa abinci; feshi, da kuma kafa tarko na mutuwa ga Ɓeraye, waɗanda sune manyan masu ɗauke da cutar.
Stow ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar kwalara a jihar.
Ya ce: “Gwamnatin jihar ta yi matukar kokari wajen ganin kowa a Bayelsa ya san muna da wata matsala wadda ita ce cutar kyandar biri. Duk da haka, muna samar da wayar da kan jama’a.
“Mun je al’ummomin inda muka tabbatar da kamuwa da cutar sankarau don yin bincike mai zurfi, ta hanyar gida zuwa gida don duba mutanen da ke da cutar sankarau don kai su cibiyar keɓewa.”