Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, ya haramta duk wani taron jama’a a fadin jihar har sai baba-ta-gani, biyo bayan barkewar sabuwar kwayar cutar COVID-19 karo na biyu.
Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Laraba, ta hannun sakataren watsa labaransa, Mr Humwashi Wonosikou a Yola, babban birnin jihar.
Ya yi nuni da cewa cutar COVID-19 gaskiya ce kuma ta zamo karfen kafa ga kiwon lafiya na duniya, amma ya nuna takaicinsa kan yadda jama’a ba sa bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar.
KARANTA WANNAN: Babbar magana: Canja ranar haihuwa a katin NIN ya koma N15,000
Dokokin sun hada da sanya makarin fuska, ba da tazara, yawan wanke hannu, kauracewa taron jama’a, amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta da dai sauransu, kamar yadda jaridar Channels TV ta ruwaito.
Gwamna Fintiri ya yi amfani da wannan dama wajen tunatar da al’ummar jiharsa matakan da aka sanya a jihar a watan Maris 2020, in da ya ce har yanzu makamanciyar wannan doka tana nan tana aiki.
1. Tilasta amfani da makarin fuska yayin da mutum zai shiga cikin jama’a ko ababen hawa.
2. Ba da tazara a cikin taron jama’a.
3. Yawaita wanke hannu tare da amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta.
4. An haramta taron nishadi kamar zuwa gidan rawa, gidajen kallo, dakin tarurrukan buki, taron ilimi da na siyasa da sauran tarurrukan jama’ar da suka wuce 100.
5. An haramta zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba.
6. Malaman addinai su kasance masu tilasta mabiyansu akan amfani da makarin fuska da kuma bayar da tazara.
Gwamna Umaru Fintiri ya yi nuni da cewa, daukar wadannan matakai ya zama wajibi ne biyo bayan sake barkewar cutar COVID-19, kuma karo na biyu na cutar ya fi hatsari akan na farko, don haka, daukar matakan zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar a cikin taron jama’a.
A wani labarin, akalla matasa masu yi wa kasa hidima karkashin shirin NYSC guda dari bakwai da talatin da bakwai (737), daga rukunin B na shekarar 2020 ne suka kamu da cutar COVID-19.
Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na dakile cutar COVID-19, Boss Mustapha ya bayyana hakan a ranar Talata.