Cibiyar dake dakile cutuka masu yaduwa ta kasa, NCDC a ranar Talata sun tabbatar da mtuuwar mutum 15 da cutar korona ta kashe, inda adadin wadanda cutar ta kashe a Nijeriya suka kai 1, 522.
NCDC sun tabbatar da hakan ne a ranar Talata. Cibiyar ta ce; an samu karin mutum 1, 303 da suka kamu da cutar, inda adadin wadanda cutar ta kama a Nijeriya ya kai 124,299.
Cibiyar ta ce an samu masu cutar ne daga jihohi 24 ciki harda birnin tarayya Abuja. Sai kuma Legas da Abuja da Nasarawa da suke dauke da dadin mai yawa wadanda suke dauke da cutar na wannan rana da adadin 478, 211, da kuma 83.