Da Ɗuminsa: Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa Nnamdi Kanu
A ranar Juma’a ne kotun koli ta amince da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
Kanu na hannun jami’an tsaro na farin kaya, DSS, tun bayan da aka sake kama shi a shekarar 2021.
A wani labarin kuma:Ƴan Majalisu Sun Jaddada Neman Wata Buƙata Ga IGP Kan Tsaro
Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan harkokin ‘yan sanda ya bukaci ministan harkokin ‘yan sanda da sufeto janar na ‘yan sanda da su dauki matakan da suka dace domin inganta harkokin tsaro a kasar nan.
Kwamitin wanda Sanata Abdulhamid Madori da kuma Sanata Abubakar Yalleman suka jagoranta, ya bayyana haka ne a lokacin da suka bayyana a gaban taron hadin gwiwa na kwamitin a Abuja domin kare kasafin kudin 2024.