Da Ɗuminsa: Kotun Koli ta tabbatar da zaben Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan Sokoto
A ranar Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da zaben Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Tijjani Abubakar ya yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar.
A wani labarin kuma:Gwamnan Zamfara Na Neman haɗin kan gwamnonin Arewa don yaƙar rashin tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada bukatar hadin kai da kuma daukar matakai daban-daban domin magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Larabar da ta gabata yayin wani taron kwana biyu da kungiyar hadin kan Arewa CNG ta shirya kan matsalar tsaro a yankin Arewa, a cibiyar samar da albarkatun kasa ta Najeriya da ke Abuja.