Da ɗuminsa: Mai Mala Buni ya miƙa ragamar Shuwagabancin APC ga Sanata Adamu
Abdullahi Adamu ya karɓi ragamar Shuwagabancin Jam’iyyar APC.
Sanatan Mai ci a halin yanzu, Masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ta kasance tsohon Gwamnan Jahar Nasarawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin jirgin ƙasa: An yi shiru na minti 1 a taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa domin karrama fasinjojin da abin ya shafa
A ranar Laraba, ya karɓi ragamar shugabancin Jam’iyyar daga tsohon Shugaban ta Mai Mala Buni a hedikwatar Jam’iyyar.
Kwamitin Riƙon Jam’iyyar APC na Gwamnan Jahar Yobe ya kasance yana jan ragamar Jam’iyyar tun Shekarar 2020.
Adamu ya kasance Shugaban Jam’iyyar a Babban Taron ta data gudanar a Eagle Square Abuja a ranar Asabar data gabata.
Sama da mutane 70 an tabbatar dasu a matsayin sabon Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar.