Rahotanni sun bayyana cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga da sanyin safiyar yau Juma’a a kusa da fadar shugaban kasar Burkina Faso da kuma hedikwatar gwamnatin mulkin sojanta, wadanda suka kwace mulki a wani juyin mulki a watan Janairun da ya gabata, kamar yadda shaidu suka shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP.
Wasu manyan tituna da dama a babban birnin kasar Ouagadougou ne sojoji suka tare kuma an katse yada shirye-shirye a gidan talabijin na kasar, inda aka watsa wani allo na cewa: “Babu siginar bidiyo”, in ji ‘yan jaridar AFP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ayu Ya Bamu Cin Hanci Miliyoyin Kudade — Ana Zargin ‘yan PDP 6 Na NWC
“Na ji karar tashin bama-bamai da misalin karfe 4:30 na safe (04:30 a agogon GMT) kuma yanzu haka motocin sojoji sun rufe hanyoyin da ke kusa da gidana,” wani mazaunin da ke kusa da fadar shugaban kasar ya shaida wa AFP.
Wani dan jarida na AFP ya ce an jibge sojoji ne a babban mararrabar birnin, musamman a unguwar Ouaga 2000 da ke da hedkwatar fadar shugaban kasa da na mulkin soja, harma kuma a wajen hedikwatar gidan talabijin din kasar.
A halin yanzu Burkina Faso dai na karkashin mulkin soja ne a karkashin Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.
Ya karbi mulki ne a watan Janairu, inda ya hambarar da zababben shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore, wanda ya kasa dakile yunkurin masu jihadi. Amma lamarin tsaro bai inganta ba.
A ranar litinin wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai hari kan ayarin motocin a arewacin kasar.
Gwamnati ta ce sojoji 11 ne suka mutu yayin da fararen hula kusan 50 suka bata.
Fiye da kashi 40 cikin 100 na kasar, wadda tsohuwar kasar Faransa ta yi wa mulkin mallaka, ba ta hannun gwamnati.
Dubban mutane ne suka mutu sannan kimanin miliyan biyu suka rasa muhallansu sakamakon fadan tun shekara ta 2015 lokacin da rikicin ya barke a Burkina Faso.
Yawancin yankin Sahel na fama da tashe tashen hankula, wanda kuma ya bazu zuwa Nijar. A cikin ‘yan shekarun nan, tashe-tashen hankula sun fara bazuwa a kasashen da ke gabar tekun Ivory Coast da Togo.AFP
A wani labarin kuma, ‘Yan sanda sun tsinci jariran da aka jefar a cikin juji a Legas
Jami’an Hukumar Kula da Sharar Sharar gida ta Jihar Legas (LAWMA) sun kwaso wani jariri a cikin juji a wani titi a Ikoyi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ya sanar da cewa an samu jaririyar ne a ranar Alhamis.