Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware yajin aikin da kungiyoyin jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin jami’o’i.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/naptip-da-wata-gidauniyar-ta-fara-horo-mai-tsauri-ga-rundunar-yaki-da-fataucin-bil-adama/
Idan dai za a iya tunawa JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran kungiyoyin ma sun janye aikinsu bayan hakan sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu.
Sauran kungiyoyin uku da suka fara yajin aikin sun hada da manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, kungiyar ma’aikatan da ba na ilimi ba, NASU da kuma kungiyar malaman fasaha ta kasa, NAAT.
Shugaba Buhari ya kira taron na ranar Talata domin karbar bayanai daga tawagar gwamnati kan yajin aikin ya dauki tsawon lokaci ana yi.
Shugaban bayan jin ta bakin masu ruwa da tsaki na MDA da abin ya shafa ya umurci Ministan Ilimi da ya tabbatar da cewa an warware matsalar cikin makonni biyu tare da kawo masa rahoto.
Majiyoyi a taron sun kuma ce shugaba Buhari ya ba da umarnin cewa ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya kasance a duk wani taron da za a yi domin warware rikicin.
Majiyar ta ci gaba da cewa, ya kamata sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha ya kasance cikin tawagar da za ta tunkari kungiyoyin da ke yajin aikin.
Daya daga cikin majiyoyin, ta ce shugaban kasar ya yabawa Ngige a kokarin da ya yi na kawo karshen takun sakar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, Ministar Kasafin kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Dakta Zainab Ahmed, Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Ngige, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani Isa Pantami, Shugabar ma’aikata ta tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan, shugaban hukumar samun albashi na kasa, Ekpo Nta, babban daraktan kasafin kudi, Ben Akabueze.