- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin babbar Akanta Janar ta tarayya.
- Rahotanni sun bayyana cewa Madein nadin nata ya fara aiki nan take.
- Oluwatoyin Sakirat ta fito daga karamar hukumar Iperu Remo Ikenne ta jihar Ogun.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin babbar Akanta Janar ta tarayya, AGF,The Nation ta rawaito.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa, Muhammed Abdullahi Ahmed ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Dage Dakatarwar Da Aka Yiwa Wasu Shugabannin Jami’iyyar LP
Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr. Folasade Yemi-Esan wadda ta sanar da nadin ta ce sabon nadin ya fara aiki nan take.
“Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr. Folasade Yemi-Esan, CFR ta bayyana hakan a yau Juma’a 19 ga watan Mayu, 2023 a Abuja, inda ta kara da cewa nadin ya fara aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, 2023.
An ce Oluwatoyin Sakirat ta fito daga karamar hukumar Iperu Remo Ikenne ta jihar Ogun kuma an haife ta ne a ranar 7 ga watan Maris shekarar 1965.
Har zuwa lokacin da aka nada ta, ta kasance Daraktar kudi da asusu a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, OHCSF.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Wanda Ya Kafa Bankin FCMB Ya Rasu
Wanda ya kafa bankin FCMB ya rasu.
Olori Omoba na Ijebuland ya rasu ne a wani asibitin Landan da safiyar Juma’a.
Marigayin ya yi bikin cika shekaru 89 a duniya a ranar 9 ga watan Maris 2023.