Crystal Palace ta sallami kocinta Patrick Vieira ranar Juma’a, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a gasar Premier wanda ya sa ta samu maki uku.
Shugaban kungiyar Steve Parish ya ce: “Abin takaici ne cewa an yanke wannan hukunci mai wahala.”
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sake Zabar Shugaban FIFA Gianni Infantino A Wa’adi Na Uku
“A ƙarshe, sakamako a cikin ‘yan watannin nan ya sanya mu cikin mawuyacin hali kuma mun ji cewa canji ya zama dole don ba mu dama mafi kyau na riƙe matsayin Premier.”
Palace, wacce ke matsayi na 12 kuma tana kan nasara daya a wasanni 14 na gasar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “ana kan aiwatar da tsarin nada sabon koci”.
Membobi uku na masu horarwar Vieira – Osian Roberts, Kristian Wilson da Said Aigoun – suma sun bar Selhurst Park.
Parish ya kara da cewa: “Patrick ya bai wa kulob din komai, kuma dukkanmu mun gode masa da tawagarsa saboda hidimar da suka yi.”
Palace ba ta yi nasara a wasan shekarar da muke ciki ta 2023 ba karkashin tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Vieira.
A wani labarin kuma, APGA Ta Musanta Narkewa A Cikin Kowace Jam’iyya
Jam’iyyar APGA a jihar Enugu ta ce ba ta ruguza tsarinta tare da narkewa ga kowace jam’iyya a jihar ba dangane da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 18 ga watan Maris.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na jihar, Ndubuisi EnechiOnyia ya fitar.