By Abbas Yakubu Yaura
Farfesa Gidado Tahir, babban sakataren zartarwa na hukumar Ilimin bai daya UBEC, ya rasu.
Cikakkun bayanai game da mutuwarsa sun kasance cikin zayyana har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Ya yi karatu a Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato da kuma Jami’ar Abuja, inda ya kai matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar kafin ya yi ritaya.
An haife shi a garin Toungo a jihar Adamawa, a ranar 29 ga watan Disambar shekarar 1949, sannan kafin rasuwar sa ya kasance shugaban hukumar (NCNE).
Marigayin ya yi karatu a makarantar sakandiren Coci of the Brethren Mission dake Waka, Biu, Borno, tsakanin shekarar 1956 zuwa 1967, sannan ya yi karatun Sakandaren Gwamnati a jihar Bauchi.
Ya kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1970. Daga nan ya halarci Jami’ar Indiana da ke Bloomington a Indiana ta kasar Amurka, inda ya samu digiri na biyu na MSc da Ph.D. a Babban Ilimi da Ci gaba.
Ya yi aiki a matsayin Shugaban kwalejin Ilimin ta tarayya dake Yola, daga shekarar 1987 zuwa 1994.
Ya rasu ya bar matarsa, Hajiya Asma’u Gidado Tahir, ‘ya’ya da jikoki da dama.