Yanzu haka dai gobara ta kone wani katafaren sashin gudanarwa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Kano.
Bayani game da lamarin yana da tsari kawo lokacin gabatar da wannan rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bambancin A Bayyane Yake: Yadda Jikin Wata Budurwa Ya Canza Watanni 3 Kacal Da Saukar A Burtaniya
An tattaro cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin kakakin rundunar ‘yan sanda PPRO, ofishin mataimakin kwamishinan (Admin), da dai sauransu.
Jaridar Dimokuradiyya ta tuntubi Jami’in hulda da jama’a na Hukumar kashe gobara Ta jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi don yin karin haske game da faruwar lamarin.
Sai dai Saminu ya bayyana mana cewa ” har yanzu suna kan tattara bayanai game da tashin wannan gobara da kuma irin asarar da tayi”.
“Zan dawo gareku da zarar mun Kammala bincike don Allah”.
A wani labarin kuma, Mijina Bai Daina Dukana Ba Duk Da Ina Taimakonsa Wajen Biya Masa Bashin Caca
Kotun Al’adu dake Mapo Ibadan a Jihar Oyo ta raba auren da wasu ma’auratan, Mariam Olalekan da Ibrahim Olalekan suka yi, bisa dalilan rashin da’a, sakaci da kuma fada da ake yi akai-akai.
Mariam, wacce ta kai mijinta kotu ta bayyana cewa ba ta da sha’awar auren, kuma ya kamata kotu ta tsinke shi.