Gwamna Muhammad Inuwa na jihar Gombe ya sha kaye a mazabar sa mai lamba 010 a unguwar Jekadafari dake cikin babban birnin jihar a hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Daily Trust ta rawaito cewa Gwamna Yahaya shi ne ko-odinetan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a yankin Arewa maso Gabas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Da Ake Zargin Masu Sayen Kuri’u Ne Sun Bude Wuta Kan Jami’an EFCC
Shugaban masu kada kuri’a PO, Misheal Thomas, wanda ya bayyana sakamakon zaben ya ce Atiku ya samu kuri’u 215 yayin da Tinubu ya samu kuri’u 186.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gwamna Yahaya ya kada kuri’arsa da rana tare da matansa Hajiya Asma’u Yahaya da Hajiya Amina Yahaya.
‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya samu kuri’u 10 yayin da Peter Obi na Labour ya samu kuri’u 4.
A wani labarin kuma, Atiku Ya Doke Tinubu A Rumfar Zabe Ta Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zabe a rumfar mazabar shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.
Daily Trust ta gano cewa Lawan wanda dan takarar jam’iyyar APC ne a jihar Yobe ta Arewa, ya kada kuri’arsa a mazabar makarantar Firamare ta Katuzu 001B.
Yayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya samu kuri’u 107, Atiku ya samu kuri’u 186.
Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP ya samu kuri’u 41, Kola Abiola na PRP ya samu kuri’u 2, Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’a 1 kacal.