Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya janye daga tsaywa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Badaru ya fice daga zaben fidda gwanin da aka shirya yi ranar litinin bayan gwamnonin APC 10 sun goyi bayan sauya shekar takarar zuwa yankin Kudu a 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Jiga-jigan Jam’iyyar APC Sun Isa Fadar Shugaban Kasa Villa Domin Ganawa Da Buhari
A yanzu haka dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana ganawa da ‘yan takarar jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Buhari, wanda ya dawo daga taron ECOWAS na musamman da aka yi sa’o’i da suka wuce, zai gana da akalla mutane 23 da aka amince da su a matsayin wadanda suke neman tsayawa takarar shugabancin kasa.
Masu fatan tsayawa takarar shugabancin kasar dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Gwamna Yahaya Bello (Kogi), Dave Umahi (Ebonyi), Kayode Fayemi (Ekiti), tsohon ministan harkokin Neja Delta, Goodwill Akpabio, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da dai sauransu.
Yayin da ya rage sa’o’i 48 a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, taron zai ta’allaka ne kan zaben dan takarar bisa tsarin yarjejeniya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban kwamitin tantancewar, Dr John Oyegun, a ranar Juma’a ya shaidawa manema labarai cewa kashi 99 cikin 100 na masu son tsayawa takara suna goyon bayan yarjejeniya.
Comments 1