Wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun jikkata bayan da jirgin fasinja ya murkushe wata motar bas din ma’aikatan gwamnatin jihar Legas a kan hanyarta daga Ikotun zuwa Alausa sakatariyar jihar a yankin PWD na jihar.
Hadarin ya afku ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓe: DSS ta bankado wani shirye-shiryen tada tarzoma
Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Taofiq Adebayo, ya ce ana ci gaba da aikin ceto.
“Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da motar bas ta cika makil da ma’aikatan gwamnatin jihar Legas da ke zuwa ofishin da safiyar yau.”
A wani labarin kuma, Wani Dan takarar Gwamna A NNPP Ya Musanta Janyewa Takwararsa Na Jam’iyar APC
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, a jihar Ebonyi, Propect Chris Adol-awam ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa ya janye takarasa ga Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC Francis Nwifuru. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Adol-awam ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abakaliki ta hannun daraktan yakin neman zabensa kan harkokin yada labarai Victor Uraku.
Adol-awam ya yi nuni da cewa, rade-radin da ake ta yadawa na janye wa ga dan takarar jam’iyyar APC, Nwifuru, wasu bata gari ne da ke son yaudarar dimbin magoya bayansa a kananan hukumomin jihar 13.
Ya caccaki ’yan siyasa da ke da hali mara kyau, kuma ya ce wasu na yin duk mai yiwuwa don ganin sun rage masa farin jini da ke kara masa daraja a matsayinsa na dan takarar gwamna a Jihar.