Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC, na shirin kaddamar da rijiyar mai ta farko a jihar Nassarawa a watan Maris din shekarar 2023, a ci gaba da aikin hako mai a cikin kasar.
Babban Jami’in Kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana haka a lokacin da Gwamnan Jihar Abdullahi Sule ya jagoranci wata tawaga ta fitattun ‘yan asalin Jihar a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa Kamfanin NNPC a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotun Koli Ta Kori Basaraken Gargajiya Na Obong, Ta Ba Da Umarnin Asake Zabar Sabon Sarki
Ministan man Fetur Mele Kyari, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ta hannun Mista Garbadeen Muhammad, Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, NNPC Ltd., ya ce sakamakon binciken da aka gudanar ya tabbatar da kasancewar albarkatun ruwan man Fetur mai yawa a jihar.
Ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan wannan aiki saboda sauyin makamashi a duniya ya haifar da raguwar zuba jari a albarkatun mai.
“Dole ne a yi wannan aikin cikin sauri saboda duk duniya tana nisa daga burbushin mai saboda canjin makamashi.
“Da farko ka je kasuwa, zai fi maka kyau, in ba haka ba, shekaru 10 daga yanzu, babu wanda zai yarda ya saka kudi a harkar man fetur sai dai daga kudaden ku,” inji shi.
Kyari ya bayyana goyon bayan al’umma da samar da yanayi mai kyau a matsayin jigon samun nasarar gudanar da aiki a yankin domin gujewa gogewar yankin Neja Delta.
A nasa martanin gwamnan ya taya GCEO murnar fara aikin hako mai da kuma aikin ci gaba na Kolmani wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Nuwambar shekarar 2022.
Sule ya ce, ”Ina son in taya ku murna, ku da mahukuntan NNPC da gwamnatin tarayya kan abin da kuka yi a Kolmani, ga wadanda ba su san abin da kuka yi wa Najeriya ba, kun rubuta sunan ku da zinari”. .
Ya yabawa shugaba Buhari bisa goyon bayan da ya bayar yayin da ya tabbatar wa kamfanin na NNPC yanayi mai kyau.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jihar Dr Emmanuel Akabe da shugaban jam’iyyar APC na kasa da gwamnan jihar na farko Dr Abdullahi Adamu da kuma tsohon gwamnan jihar Sanata Tanko Almakura.
Sauran sun hada da Ministan Muhalli, Mista Mohammed Abdullahi, Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Muhammad, da Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC), Malam Isa Modibo, da dai sauransu.NAN
A wani labarin kuma, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna Ya Fice Daga APC Zuwa Jam’iyyar LP
Gabanin zaben 2023, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Isaac Auta ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a jihar ya koma jam’iyyar Labour LP.
Kazalika karin wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zaria Suleiman Dabo ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar LP.