Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta dage sauraren karar zuwa ranar Laraba mai zuwa 17 ga watan Mayu,Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Osun
Idan za’a iya tunawa JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi su suka shigar da karar kan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
Kotun dai ta dauki matakin ne kan bukatar dage zaman da bangarorin da suka shigar da kara suka yi.
A wani labarin kuma,Guda Daga Cikin Jam’iyun Adawa Ta Janye Karar Da Ta Shigar Da Tinubu
Jam’iyyar Action Peoples Party na neman janye karar da ta shigar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lauyan jam’iyyar APP, Obed Agu, ya kuma roki kotun da ta yi watsi da karar da ke kalubalantar nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kana Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, SAN, bai kalubalanci kudurin da takwaranshi ya shigar ba.
Daga bisani Alkalin Kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya yi watsi da karar.
Idan zaku iya tuna wa cewa, kotun ta fara zaman sauraren karar ne a Abuja ranar Litinin.