Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, babban birnin tarayya a ranar Alhamis ta amince da daukaka karar da ake tsare da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.
Kotun ta kuma sallame shi tare da wanke shugaban haramtacciyar kungiyar da aka kama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wike: Na Amince Da Atiku Amma Dola Ne Ayu Yayi Murabus
Lauyan Kanu kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Ifeanyi Ejiofor, ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
“An amince da daukaka kara, Oyendu Mazi Nnamdi KANU, an kuma sallame shi. Mun yi nasara! ” ya rubuta.
Kanu ya shigar da kara a ranar 29 ga watan Afrilu mai lamba CA/ABJ/CR/625/2022, inda ya nemi a sake shi kuma a wanke shi.
An fara gurfanar da Kanu a gaban kotu a ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2015, sannan aka bayar da belinsa a ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2017.
A wani labarin kuma, Kamfanin Mai Na NNPC Shine Babbar Matsalar Najeriya — Gwamna El-rufa’i
gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi matukar gazawa a harkar man fetur da iskar gas don haka ya kamata ta fice daga bangaren.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wurin taron shekara-shekara na KADINVEST wanda hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya.