Paris St-Germain ta sayi dan wasan baya Lucas Hernandez mai shekaru 27 daga Bayern Munich kan kudi fam miliyan 34
Wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a 2018 tare da Faransa, Hernandez ya lashe kofuna uku da Bayern a 2019-20 – kakarsa ta farko a kulob din
Bayan da Hernandez ya lashe gasar lig da kofin gida biyu, Hernandez ya taimaka wa kungiyar Hansi Flick ta doke PSG ta lashe gasar zakarun Turai
Hernandez, wanda ya buga wa zakarun Bundesliga wasanni 107 kuma ya zura kwallaye biyu, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar a PSG
KARANTA NANBa Rashin Daukar Kiran Tinubu Yasa Muka Kama Yari Ba-DSS
Na yi farin ciki sosai,in ji Hernandez na dade ina jiran in koma PSG, kuma daga karshe abin ya faru, rana ce ta musamman a gare ni kuma ina matukar farin cikin kasancewa a nan
Ya taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin duniya da Faransa ta lashe a Rasha a 2018, amma duk da cewa an zabe shi a Les Bleus a gasar cin kofin duniya a Qatar 2022
Raunin gwiwa da ya samu a wasansu na uku na rukuni inda suka tashi 4-1 da Australia – ya sa aka fitar da shi daga tawagar sai kuma aka maye gurbinsa da kanensa
Sun kai wasan karshe na gasar karo na biyu a jere, amma Argentina ta doke su a bugun fenariti
Kanensa, Theo Hernandez, yana taka leda a AC Milan ta Seria A inda shima yake buga gefen mai tsaron baya
A WANI LABARIN KUMA
Bayan Shafe Shekaru 12 David De Gea Ya Bar Manchester United
Mai tsaron ragar Manchester United David Degea dan asalin kasar Sifaniya ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar bayan shafe shekaru 12 a Old Trafford
Degea ya bayyana aniyarsa ta barin Man Utd a shafinsa na Twitter inda ya kira kungiyar da jininsa kuma ba zata taba fita daga ransa ba har abada