A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta amince da kudirin kasafin kudin shekarar 2023, inda ta kara kiyasin kasafin Naira Tiriliyan 20.51 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar zuwa Naira Tiriliyan 21.82. Kamar yadda Daily Trust Ta ruwairo.
Kasafin kudin da aka amince da shi ya nuna karin sama da Naira tiriliyan 1 na alkaluman da bangaren zartaswa ta gabatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Farashin Zinari Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Masar
Matakin ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar a zauren majalisar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: IG Ya Dakatar Da Dan sandan Da Ake Zargi Da Harbe Lauya
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya bayar da umarnin dakatar da Drambi Vandi nan take, dan sandan da ake zargi ya harbe Bolanle Raheem.
Mataimakin Sufeton ‘yan sandan yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Ajiwe da ke karkashin hedikwatar shiyyar Ajah na rundunar ‘yan sandan jihar Legas.
Vandi ya harbe Bolanle, wata lauya mai juna biyu a ranar Lahadi.
Marigayiyar da ‘yan uwanta na kan hanyarsu ta zuwa gida ne bayan siyayyar ranar Kirsimeti.