Yanzu haka dai fitacciyar kasuwar Agbeni da ke garin Ibadan a jihar Oyo tana ci da wuta.
PUNCH ta tattaro cewa kasuwar ta kama da wuta da misalin karfe 04:30 na safiyar ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mummunar Gobara Ta Kone Shaguna 150 A Kasuwar Zariya
Da aka tuntubi babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar, Yemi Akinyemi ta wayar tarho, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.
Akinyemi ya ce, “Hukumar ta samu wannan kiran ne da misalin karfe 04:37 na safe ta bakin wani Sunday Ogundele, jami’an tsaro na bankin Access inda ya sanar da tashin gobarar a kasuwar Agbeni.
“Jami’anmu har yanzu suna fama da aikin kashe wutar, muna godiya ga Babban Bankin Najeriya da ya ba mu damar amfani da ruwansu. Komai yana karkashin iko.”
“Har yanzu suna zuwa CBN don sake kwaso ruwan,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Mummunar Gobara Ta Kone Ginin Wata Hukuma
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta tabbatar da afkuwar tashin gobara a ofishinta da ke jihar Enugu.
Gobarar ta cinye ɗaya daga cikin gine-ginen ofishin hukumar da ke yanki.
Shugaban yada labarai na EFCC, Wilson Uwujaren shine wanda ya fitar da sanarwar da yammacin ranar Juma’a.