Kungiyar kwallon kafa da Paris Saint Germain ta sanar da daukar sabon kocin da zai jagoranci Kungiyar a kakar wasa ta badi
PSG ta dauko tsohon kocin Fc Barcelona kuma wanda ya jagoranci tawagar kwallon kafa ta kasar Sifaniya a gasar cin Kocin Duniya da aka kammala a kasar Qatar Luis Enrique
PSG ta sanar da daukar Enrique a matsayin sabon koci wanda zai maye gurbin Christopher Galtier wanda ya jagoranci kungiyar ta Faransa tsawon kaka daya
Galtier wanda ya zo PSG a bara daga kungiyar Lille ya kasa tabuka abin azo a gani a kungiyar ta birnin Paris bayan an kori kungiyar daga gasar zakarun Turai ta Uefa Champions League
KARANTA NANDaga Karshe Manchester United Ta Dauki Mount Daga Chelsea
Enrique ya taka lashe gasar zakarun Turai ta Uefa Champions League a shekarar 2015 lokacin da yake jagorancin kungiyar kwallon kafar Fc Barcelona ta kasar Sifaniya
Muna sanar da daukar gogaggen koci kuma wanda yasan harkar kwallon kafa a Turai Luis Enrique domin zama Sabon kocin da zai jagorance mu tsawon shekaru biyu inji PSG
Muna fatan samun nasara tare da Enrique wanda ya nunawa Duniya abin da zai iya a harkar kwallon kafa tsawon shekaru da ya kwashe a matsayin koci
A WANI LABARIN KUMA
Gwamnan Jahar Neja Yayi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Fadar Sarkin Minna
Gwamnan Jahar Neja Malam Umar Bago ya yi Allah wadai da wani harin bindiga da aka kai fadar mai martaba sarkin Minna Alh Umar Farouk Bahago a Minna fadar gwamnatin Jahar
Bazamu lamunci hare haren yan bindiga a Jahar Neja ba matukar muna rike da madafun iko inji gwamnan ta hannun babban mai taimaka masa akan harkokin watsa labarai Malam Bologi Ibrahim