Iyalan Afegbua sun sanar da mutuwar Sanata Franca Afegbua a wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi.
“Iyalan Afegbua na jihar Edo sun tabbatar da rasuwar mace ta farko wacce ta zama ‘yar majalisar dattawa a Najeriya, Sanata Franca Afegbua, wanda lamarin bakin ciki ya faru a safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Maris, 2023.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Daina Kame Mambobinmu Ko Mu Mamaye Ofisoshin Ku – PDP Ta Gargadi ‘Yan Sanda
“Ta hada kyau da kwakwalwa a lokacin da ta yi hidimar Najeriya. Iyalin za su sanar da bayanan jana’izarta nan ba da jimawa ba,” in ji dangin.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa an zabe ta a matsayin sanata mai wakiltar Bendel ta Arewa a watan Oktobar shekarar 1983 karkashin jam’iyyar National Party of Nigeria NPN a jamhuriya ta biyu ta Najeriya.
Afegbua, mai shekaru 79, ‘yar asalin Okpella ce, wani gari a karamar hukumar Etsako ta Gabas ta tsohuwar jihar Bendel, yanzu ta rabu zuwa jihohin Edo da Delta.
Duk da haka, tafiyar siyasarta ta katse yayin da juyin mulkin soja na watan Disambar shekarar 1983 ya hambarar da gwamnatin farar hula kasa da watanni uku bayan da ta karbi mulki.
A wani labarin kuma, Messi Ya Kafa Wani Tarihi Bayan Nasarar Da PSG Ta Samu
Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain, Lionel Messi, a ranar Asabar ya zama dan wasa na farko da ya taimaka wa kungiyoyi 300.
Messi ya samu wannan nasarar ne bayan da ya kafa wa abokin wasansa Kylian Mbappe wanda ya yi nasara a wasan da suka doke Brest da ci 2-1 a gasar Lig 1 ta Faransa ranar Asabar.