- Shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya rantsar da kwamishinonin gwamnatin tarayya guda bakwai.
- An gudanar da bikin ne a gaban taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.
- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin kawo sauyi kan harkokin lafiya ga shugaba Buhari.
- A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya rantsar da kwamishinonin gwamnatin tarayya guda bakwai na hukumar tara kudaden shiga, rabon kudi da kuma kasafin kudi,Punch ta rawaito.
An gudanar da bikin ne a gaban taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.
KARANTA WANNAN: Zaɓaɓɓen Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani Ya Nada Sakataren Yada Labaran sa
Sabbin kwamishinonin gwamnatin tarayya da aka nada sune Sanata Ayogu Eze (jihar Enugu); Peter Opara (Jihar Imo); Hawa Aliyu (Jihar Jigawa); Rekiya Haruna (jihar Kebbi);
Sauran sune Ismaila Agaka (Jihar Kwara); Kolawole Abimbola (Jihar Oyo); da Hauwa Aliyu (Jihar Jigawa); da Ayuba Ngako, wanda zai zama wakilin babban birnin tarayya.
A halin da ake ciki mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin kawo sauyi kan harkokin lafiya ga shugaba Buhari.
Kwamitin wanda Osinbajo ke jagoranta, an kafa shi ne domin samar da taswirar cimma nasarar tsarin kiwon lafiya na duniya a kasar.
Daya daga cikin muhimman shawarwarin da kwamitin ya bayar shi ne inganta kudaden tallafi ga fannin kiwon lafiya.
A wani labarin kuma,Na Yafewa Shugaba Buhari, Inji Gwamnan PDP
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce ya yafewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Gwamnan yace “Idan ba ku yafe ba, yana nufin Allah ma ba zai gafarta muku ba.
Ortom dai ya sha sokar fadar shugaban kasa kan zargin gwamnatinsa da kashe kashen da ake yi a jiharsa.