- Shugaban tarayyar Najeriya Tinubu zai halarci taron kasashen G-20 da zai gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya
- Babban burin Tinubu a taron shi ne jawo jarin kasashen waje zuwa Najeriya daga sassa daban-daban na duniya don tallafawa ci gaban kayayyakin more rayuwa a kasar
- Taron na da nufin tinkarar manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya da daidaiton kudi na kasa da kasa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu na shirin halartar taron kasashen G-20 da zai gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Satumba.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Gwamna Bago Ya Ayyana Hutun Kwanaki Uku Don Raba Kayan Tallafin Abinci
Ngelale ya bayyana cewa babban burin Tinubu a taron shi ne jawo jarin kasashen waje zuwa Najeriya, yana mai jaddada muhimmancin tara jari masu zaman kansu daga sassa daban-daban na duniya don tallafawa ci gaban kayayyakin more rayuwa a kasar.
G-20, wanda kuma ake kira Rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, taron gwamnatoci ne da ya kunshi kasashe 19 da Tarayyar Turai.
“Ana da nufin tinkarar manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya, kamar daidaiton kudi na kasa da kasa, rage sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa.
Kungiyar ta kunshi kasashen Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Koriya ta Kudu, Japan, Mexico, Rasha, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Burtaniya, Amurka, da kuma Tarayyar Turai.
Ngelale ya kara da cewa, an shirya shugaba Tinubu zai tattauna da shugabannin duniya, shugabannin kasashe, shugabannin masana’antu, da manyan jami’an fitattun kamfanoni, musamman wadanda suka samo asali daga kasar Indiya.
“Za mu tabbatar da cewa, a karkashin jagorancin shugaban kasa, mun yi amfani da damar da muka samu wajen kara wa al’umma kimar kasa, da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, da kuma kara habaka da samar da albarkatu domin al’ummar kasar nan su lamunce cewa gwamnati za ta iya samar da kudade yadda ya kamata tare da tallafawa shirye-shiryenta na gaba.
“Akwai abubuwa da yawa da za mu iya kawowa, kuma idan muka shigo Najeriya a mako mai zuwa, za a rika samun labarai kai tsaye daga Indiya, wadanda zan samar da su a kowace rana don baiwa ‘yan Najeriya cikakkiyar damar sanin abin da shugabansu ke yi a madadinsu,” inji shi.
A wani labarin kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Taya Shettima Murnar Bikin Cikarsa Shekaru 57
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya yaba da kyawawan halayen mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasar kafin ya shiga fagen siyasa ya kasance ma’aikacin banki, inda yake bayar da gudunmawa sosai wajen tabbatar da dimokuradiyya
Shettima ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin cikin gida ya yi aiki tukuru don magance kalubalen da hukumomi ke fuskanta a karkashin kwamitinsa
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya yaba da kyawawan halayen mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, a yayin bikin cikarsa shekaru 57 a duniya.
Sanata Barau, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ismail Mudashir ya fitar ya ce;