Southampton ta kori kocinta, Nathan Jones, bayan ta sha kashi a hannun Wolves da ci 2-1 a ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu, LIB ta rawaito.
Sallamar Jones a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ke ci gaba da tabarbarewa a kasan teburi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Duminsa: DSS Ta Gayyaci Fani-Kayode Kan Rahoton Juyin Mulki
Kungiyar ta Premier ta kuma kori kocin kungiyar ta farko, Chris Cohen da Alan Sheeha.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na yanar gizo.
Sanarwar ta kara da cewa,
Kungiyar Kwallon Kafa ta Southhampton na iya tabbatar da cewa ta raba gari da Manajan Tawagar Maza Na Farko Nathan Jones.
Kocin farko Chris Cohen da Alan Sheehan suma sun bar kungiyar.
Mai horar da kungiyar ta farko dan wasanta Rubn Sell zai dauki nauyin atisaye tare da shirya kungiyar gabanin wasan da za ta yi da Chelsea a karshen mako mai zuwa.
A wani labarin kuma, Sanata Ahmad Lawan Ya Musanta Rahoton Tashin Hankali Da Ake Yadawa A Mazabar Yobe Ta Arewa
A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce rashin gaskiya ne da kuma kage-kage da aka yi cewa taron yakin neman zaben jam’iyyar APC na shiyyar Gashua da ke karamar hukumar Bade a jihar Yobe ya fuskanci tashin hankali.
Lawan, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi ya fitar ranar Lahadi a Abuja, yana mayar da martani ne kan rahotannin da kafafen yada labarai suka ruwaito na samu tashin hankalin a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairu, 2023.