- Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi ya shiga cikin wata ganawar sirri da shugaba Bola Tinubu
- Duk da cewa har yanzu ba a san cikakken bayanin ganawar da ake yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja ba, amma duk da haka bai rasa alaka da ganawar Sanusi da gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar
- Ganawar ta Sanusi ta zo ne bayan da gwamnatin mulkin soja ta ki amincewa da ganawar da aka shirya yi da wakilan kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da ECOWAS, da jami’an diflomasiyya na Amurka
Fadar shugaban kasa dake Abuja – A daren ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi suna wata ganawa a fadar shugaban kasa dake Abuja, kamar yadda Legit.ng ta rawaito
Ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sanisu ya gana da shugabannin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Sarki Sanusi Ya Gana Da Jagororin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar
Sanusi dai ya dawo daga Jamhuriyar Nijar bada jimawa ba inda ya je ya gana da gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki daga hannun zababben shugaban kasa Muhamad Bazoum.
Sanusi Lamido Sanusi ya isa fadar shugaban kasa ne da misalin karfe 8:25 na dare kai tsaye bayan wata tawagar Malamai ta Najeriya ta gana da shugaban.
Da aka tambaye shi game da ziyararsa a Nijar, sai kawai tsohon Sarkin ya ce, ba komai.
Kawo yanzu dai zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, Sanusi na ci gaba da ganawa da shugaban kasar.
A wani labarin kuma, Ƙirƙirar Jiha: Majalisar Dattawa Zata Yiwa Kowa Adalci a Sake Fasalin Kundun Tsarin Mulki – Barau
Gabanin wani shirin sake duba kundin tsarin mulki, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatar wa ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa jihohin Tiga da Gari daga jihar Kano cewa majalisar za ta yi wa kowa adalci a lokacin sake duba kudin tsarin mulkin shekarar 1999.
Sanata Barau ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan kungiyar karkashin jagorancin Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa suka kai masa ziyarar ban girma a zauren majalisar a ranar Laraba.