Hukumar shirya jarrabawar Afrika ta yamma WAEC, ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantun sakandare ta yammacin Afrika ta 2023 (WASSCE).
Hukumar jarrabawar ta fitar da sakamakon ne a ranar Litinin, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Borno: Zulum Ya Amince Da Daukar Ma’aikatan Lafiya Sama Da 50
Patrick Areghan, shugaban ofishin Najeriya (HNO) na WAEC, ya ce daga cikin mutane 1,613,733 da suka zana jarabawar, an hana sakamakon ‘yan takara 262,803 “Saboda rahotannin da aka samu na magudin jarabawar.”
Ya ce an samu ci gaba a fannin samun gurbin karatu a matsayin jimillan mutane 1,361,608, masu wakiltar kashi 84.38 cikin 100, sun samu kiredit da sama da haka a mafi karancin darussa biyar masu dauke da harshen Ingilishi ko lissafi.
Haka kuma, ’yan takara 1,287,920, wadanda ke wakiltar kashi 79.81 cikin 100 na jimlar ’yan takarar, sun samu kiredit da sama da haka a cikin mafi karancin darussa biyar, da suka hada da Ingilishi da Lissafi.
A wani labarin kuma, Gwamna Abba Ya Rantsar Da Babbar Alkaliyar Alkalai Mace Ta Farko A Kano
Sabuwar babbar alkaliyar alkalai ta yi alkawarin dawo da martabar bangaren shari’a.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da mai shari’a Dije Audu Aboki a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar alkalai a jihar.
Bikin ya gudana ne a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin din nan, inda gwamna Yusuf ya bukaci bangaren shari’a da su marawa kokarin gwamnatin sa na ruguza gine-gine da kuma kwato kadarorin al’umma da ake zargin gwamnatin da ta shude ta samu ta hanyar da ta saba doka.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati uku.