Wani jirgin yaki mallakar rundunar sojin saman Najeriya a ranar Juma’a ya yi hatsari a garin Makurdi na jihar Benue, kamar yadda Punch ta rahoto.
Cikakkun bayanai game da faruwar lamarin har yanzu suna cigaba da zayyana har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Wani Basaraken Gargajiya Ya Ziyarci Tinubu A Aso Rock
Wata majiyar soji ta ce wasu jami’an rundunar sojojin saman Najeriya biyu da ke cikin jirgin sun yi nasarar fita ba tare da sun ji rauni ba.
Majiyar ta ce, “Jirgin FT7-NI ya yi hatsari a yau a Makurdi. Har yanzu dai ba a iya gano musabbabin faruwar hatsarin jirgin ba.
“Akwai matuka jingin guda biyu a cikin jirgin, Sun fita ba tare da sun jin rauni ba.”
Kakakin hukumar, Air Commodore, Edward Gabkwet, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin horo, inda ya kara da cewa matukan jirgin suna “karkashin kularwar likitoci” a asibitin NAF Base.
Gabkwet, ya ce babban hafsan hafsoshin sojin sama ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin faruwar hatsarin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Jirgin horar da sojojin saman Najeriya FT-7NI ya yi hatsari a yau, 14 ga watan Yuli, 2023 da misalin karfe 4.15 na yamma a garin Makurdi na jihar Benue, a lokacin da yake atisayen horo.
“An yi sa’a, matukan jirgin guda 2 da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin.
“Bugu da ƙari, babu mace-mace ko lalacewa a yankin da abin ya shafa.
“A yanzu haka duka matukan jirgin biyu suna karkashin kulawa a asibitin NAF Base dake Makurdi.
“A halin da ake ciki, babban hafsan hafsoshin sojin sama, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin faruwar hatsarin nan take da kuma nesa.”
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a cikin watan Fabrairun 2023 jirgin sojojin sama ya yi asarar rasa tayar sa a lokacin da yake sarararin samaniya inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Legas ba tare da samun asarar rai ba.
Har ila yau, a watan Afrilun 2022, wani jirgin sama mai ba da horo ya yi hatsari a Kaduna, inda ya hallaka matukan jirgin guda biyu.
A wani labarin kuma, Tinubu Zai Shilla Zuwa Birnin Nairobi Domin Halartar Taron AU
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya a ranar Asabar, 15 ga watan Yulin da muke ciki domin halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na biyar (5thMYCM) na kungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Kakakin shugaban kasar, Dele Alake, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’ar nan, ya ce shugaban a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS zai hadu da shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci, ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AU.