- Wasu fusatattun matasa, a safiyar Lahadi 28 ga watan Mayu, sun rufe gidan Rediyon Najeriya, Amuludun FM 99.1.
- Fusatattun matasan sun yiwa tashar gidan radeyon kawanya ne da nufin daukar nauyin gudanar da shirin.
- Batare da bata lokaci ba jami’an tsaro masu tsattsauran ra’ayi sun fatattake su daga gidan radiyon.
Wasu fusatattun matasa, a safiyar Lahadi, sun rufe gidan Rediyon Najeriya, Amuludun FM 99.1 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Wata majiya ta shaidawa jaridar PUNCH cewa matasan sun yiwa tashar kawanya ne da nufin daukar nauyin gudanar da shirin.
KARANTA WANNAN: Bankwana: Na Bar Sahihan Tsarin Zabe – Buhari
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa jami’an tsaro masu tsattsauran ra’ayi sun kore su daga tashar gidan radiyon.
Gidan rediyon wanda yake a madakatar J&P, Moniya dake Ibadan, karamar hukumar Akinyele ta jihar, an kafa shi ne a ranar 10 ga Oktobar shekarar 2007.
Sannan kuma ya fara watsa shirye-shirye cikin harshen Yarabanci tsantsa a ranar 22 ga watan Oktobar shekara.
A wani labarin kuma, Ku Rungumi Ƙaddara A Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yi
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci jam’iyyun adawa da su amince da hukuncin da kotun ta yanke.
“Ina kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su amince da hukuncin kotunan mu, mu hada karfi da karfe don gina Najeriya mai inganci.”
Buhari yace “A yayin yakin neman zabe, mun yi ta muhawara da rashin jituwa kan yadda za a inganta Najeriya amma ba mu taba samun sabani ko kuma shakkun cewa dole ne Najeriya ta samu ci gaba ba.