Da Dumi-Duminsa: An Gano Jaririn Da Aka Sace A Kasuwar Neja
An gano wani jariri dan wata shida mai suna Chinedu Chukwueke da aka sace a shagon mahaifiyarsa da ke kasuwar kure, Minna, babban birnin jihar Neja.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, mahaifin yaron, Chikezie Stanley Chuks, ya bayyana hakan a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:INEC Na Neman Shawarwari Ga Yan Najeriya Kan Yadda Zata Rika Gudanar Da Zabe
Ya ce an jefar da jaririn ne a wani juji da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na Gauraka a karamar hukumar Tafa a jihar Neja.
Daily Trust ta ruwaito cewa wani ne ya dauke jaririn daga shagon mahaifiyarsa wanda ya yaudari mahaifiyar da take son ta koyi gyaran gashi.
“An sami jariri. An jefar da shi a wata juji da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na Gauraka. Yarinyar na cikin koshin lafiya,” ya sanar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cewa an gano jaririn ne a ranar Laraba da misalin karfe 12:30 na rana.
Ya ce, “Saboda ci gaba da matsa lamba da kuma sanya ido sosai, an gano jaririn a yashe a wani rami mai zaizayar kasa, kusa da makarantar firamare ta Gauraka a karamar hukumar Tafa.”
Ya ce an kai jaririn wani asibiti da ke kusa don duba lafiyarsa, kuma an tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya, daga nan kuma ya sake haduwa da iyalan.
Ya ce ana ci gaba da kokarin cafke wanda ya aikata laifin da ya gudu domin fuskantar fushin doka.
A wani labarin kuma:Ana Cigaba Da Fargaba Kan Yunkurin Juyin Mulki A Nijar
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, Laraba ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan “yunkurin juyin mulki a Nijar.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta yi kira ga masu yunkurin juyin mulkin da su sako zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum.