Tambarin jam’iyyar Labour LP ya bace a cikin takardun zaben da aka aika jihar Ondo.
An lura da hakan ne kawai sa’o’i 24 kafin zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.
KU KARANTA KUMA Jam’iyyar LP Ta Koka Kan Yadda INEC Ta Hana Matasa Hakkinsu
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Jam’iyyar Labour LP ita ce mai dan takarar shugaban Kasa Peter Obi wanda masu fashin bagi da sharhi ke ganin yana cikin yan takara 4 da zasu iya cin zabe.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan lafin fara gudanar da babban zaben shugaban Kasa da na yan majalissun Kasa.
A Wani Labarin Kuma FG Ta Bada Umarnin Aiwatar Da Sabbin Manufofin Bizar Amurka
Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin ci gaba da aiwatar da sabon tsarin daidaita ma’amalar biza ga ‘yan kasar Amurka daga ranar 1 ga watan Maris na 2023.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce an bayar da umarnin ne biyo bayan amincewa da aiwatar da sabbin yarjejeniyoyin tsare-tsare na ofishin jakadanci tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.