By Abbas Yakubu Yaura
Firaministan kasar Kanada Justin Trudeau, a ranar Litinin, ya bayyana cewa an gwada shi ya kamu da cutar COVID-19.
Trudeau ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter da aka tabbatar, yayin da ya kawar da fargabar mutanen Kanada da kalmomin, “Ina jin dadi.”
Dan siyasar mai shekaru 50 ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da aiki daga nesa yayin da yake bin ka’idojin kiwon lafiya da aka samar a kasar.
Firaministan ya kuma karfafa gwiwar ‘yan kasar da su sami rigakafin COVID-19 da allurar kara kuzari.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter, “A safiyar yau,an gwada ingancin jikina kuma an sameni ina dauke da COVID-19.
Ina samun lafiya – kuma zan ci gaba da yin aiki daga nesa a wannan makon yayin bin ka’idodin lafiyar jama’a. Kowa, don Allah a yi masa alluran rigakafi kuma a ƙara ƙarfafawa.”
Cutar COVID-19 dai tayi kamari awasu kasashen duniya wajen fafutukar ganin sun kawo karshenta ta hanyar yin rigakafi.