By Abbas Yakubu Yaura
Babban jami’in Twitter Jack Dorsey ya yi murabus, mista Dorsey, mai shekaru 45, wanda ya kafa kamfanin a shekarar 2006, ya sanar da murabus din nasa a wani sako daya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Sannan yace “a karshe lokaci ya yi da zan tafi”, ya kara da cewa “domin na yi imanin kamfanin a shirye yake ya ci gaba daga wadanda suka kafa shi”.
Parag Agrawal, tsohon Babban Jami’in Fasaha na rukunin yanar gizon microblogging, shine wanda aka sanar a matsayin sabon Shugaban kamfanin.
A cikin wani sakon Twitter, Agrawal ya godewa Dorsey da kungiyar Twitter da suka zabe shi a matsayin sabon shugaba na kamfanin.
Ina mai “Mika godiya ga @jack da dukan ƙungiyarmu, da kuma farin ciki ga nan gaba. Ga takardar dana aika wa kamfani. Ina godiya saboda amincewa da goyon bayanku.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A cewar Sky News, hannun jarin kamfanin Twitter ya karu bayan samun rahoton cewa Dorsey zai bar aikinsa.inda tuni Hannun jari a dandalin sada zumunta ya karu da kashi 9% a kasuwar da aka bude ranar Litinin da safe.
An dakatar da ciniki a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York bayan tashin gwauron zabi, amma an koma cinikin hannun jari tare da samun sama da kashi 4.5% gabanin inda suka bude.
Dorsey ya ci gaba da zama Shugaban Kamfanin biyan kudi na Square, wanda ke da jarin kasuwa sama da dala biliyan 98 (£ 73bn) idan aka kwatanta da dala $ 38bn na Twitter (£ 28bn).