Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Babban Akanta Janar na Tarayya, Idris Ahmed tare da wadanda ake tuhumarsa bisa sharuddan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati ta bayar.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeyemi Ajayi ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan suna so sai sun nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/buhari-bai-san-da-barazanar-yan-taadda-na-sace-shi-ba-sai-da-na-sanar-da-shi-el-rufai/
Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi sharuddan belin da EFCC ta gindaya.
Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ka ga su sayi fasfo na daban, har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar EFCC.
Alkalin kotun ya bayar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.
Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda ake tuhumar ana da damar bayar da belinsu, duk da zargin da ake yi musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC.
An fara shari’a kai tsaye bayan yanke hukuncin neman beli.