By Abbas Yakubu Yaura
Mutane da dama ne suka mutu a wani mummunan hatsarin da ya afku a ranar Alhamis a kan hanyar Bauchi zuwa Jos, kamar yadda jaridar Dimokuradiyya ta rawaito.
Duk da cewa har yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu a hatsarin ba, hotunan da aka aiko wa Wakilinmu daga inda lamarin ya faru ya nuna gawarwaki hudu kwance a kasa.
A cewar rahotanni, Motar Hummer Bas da Sharon Bas ne suka shiga cikin lamarin. An gano cewa daya daga cikin motocin da lamarin ya shafa ta kama wuta kuma tana ci gaba da konewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a wata tattaunawa ta wayar tarho, Sai dai ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba.
“Eh, an samu wani hatsari da yammacin yau a kewayen garin Buzaye da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos. A yayin da nake magana da ku, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wurin da hatsarin ya afku.
“Don haka, ba zan iya gaya muku ainihin adadin mutanen da suka mutu ba. Bayan aikin ceto, zan yi muku cikakken bayani,” in ji Abdullahi.