Rahotanni sun bayyana cewa dukkan ‘ya’yan tsohon Akanta Janar na Jihar Zamfara, Abubakar Bello Furfuri da aka sace sun shaki iskar ‘yanci.
An sake su ne a ranar Litinin, watanni biyar bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ibrahim Usman Ya Lashe Tikitin Sanatan Kaduna Ta Tsakiya A Sabon Zaɓen Da PDP Ta Canza
An sace ‘yan matan da sauran su ne a daren ranar 5 ga watan Yuni a unguwar Furfuri da ke karamar hukumar Bungudu.
Mazauna kauyen sun tabbatar da cewa an kama mutane kusan 20 a yayin harin kafin jami’an tsaro su isa.
Daga karshe an bar ‘yan matan su fice daga dajin bayan an biya makudan kudade a matsayin kudin fansa, inji rahoton PRNigeria.
A cikin watan Oktoba, Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito masu garkuwar sunyi barazanar auren wadanda aka yi garkuwa da su idan ba a biya musu bukatunsu ba.
A wani labarin kuma, Diyar Ekweremadu Ta Bayyana A Gaban Kotu A Kasar Birtaniya Bisa Zargin Safarar Bil’adama
Sonia diyar dan majalisar dokokin Najeriya, Ike Ekweremadu, ta gurfana a gaban kotu bisa zargin safarar wani matashi zuwa kasar Burtaniya domin cire wani bangare na sassan jikin sa.
Kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito, an zargi Sonia ne tare da mahaifinta Ekweremadu mai shekaru 60 da mahaifiyarta Beatrice Ekweremadu mai shekaru 56 da kuma likita Obinna Obeta mai shekaru 50 da laifin hada baki wajen shirya tafiyar wani da nufin yin amfani da shi.