Ameerah, diyar Malamar Kaduna Kadpoly da aka sace, Dakta Ramatu Abarshi, ta samu ‘yanci bayan ta shafe kwanaki 38 a hannun ‘yan bindiga.
A ranar Talata aka sake ta kuma an kaita wani asibiti da ba a bayyana ba domin a duba lafiyarta, a cewar wata majiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa an sace Dr Abarshi, diyarta da direban su, Ibrahim a ranar 24 ga Afrilu, 2022, a kan babbar hanyar Kachia zuwa Kaduna a lokacin da suke dawowa daga aikin agaji.
Yayin da aka sake mahaifiyar yarinyar kimanin makonni uku da suka gabata, direban ya sake samun ‘yancinsa a makon da ya gabata yayin da aka sako ‘yar bayan kwanaki biyar da sakin direban.
“Eh, an sako ‘yar Ameerah ranar Talata da yamma; ta sake haduwa da ‘yan uwanta kafin a kaita wani asibiti da ba a bayyana ba domin kula da lafiyarta.
” Ba abu ne mai sauki ba amma mun gode wa Allah ta dawo gida lafiya,” inji shi.
Majiyar ta shaida wa Jaridar Daily trust cewa masu garkuwa da mutanen sun karbi kudin fansa da ya kai miliyoyi naira kafin sakin mutanen