By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya isa Abuja daga kasar Habasha inda ya halarci zaman taron shugabannin kasashen Afirka karo na 35.
Kafin ya bar kasar Habasha, shugaban ya karbi bakuncin mataimakiyar babbar sakatariyar Majalissar Dinkin Duniya Amina Mohammed a gefen taron kungiyar AU.
Ya kuma karbi bakuncin Mataimakin Sakatare-Janar da kuma Mataimakin Gudanarwa, Darakta, da Ofishin Shirye-shiryen ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka, Ahunna Eziakonwa.
A jiya ya gana da babbar minista da kuma ministar harkokin wajen kasar Guinea-Bissau, Suzi Barbosa, wadda ta gabatar da jawabai kan yunkurin hambarar da kundin tsarin mulkin kasarta.
A yayin ganawar da ministan ta Guinea-Bissau, shugaba Buhari ya yi alkawarin tuntubar sauran shugabannin kungiyar ECOWAS kan yadda za a dawo da zaman lafiya a kasar cikin kankanin lokaci.