Babban bankin Nigeria (CBN) ya umurci dukkanin bankunan ajiyar kudade (DMBs, cibiyoyin hada hadar kudade da ba bankuna ba (NBFIs) da kuma sauran cibiyoyin hada hadar kudade (OFIs) da su rufe asusun mutanen da ke kasuwancin Crypto currency a Nigeria.
Babban bankin a cikin wata takarda mai taken BSD/DIR/GEN/LAB/14/001 da ya fitar a ranar Juma’a, ya umurci dukkanin cibiyoyin hada hadar kudaden “da su gano mutane ko kungiyoyin da ke hada hadar kudade ta hanyae crypto currency a cibiyoyinsu tare da kulle asusun su ba tare da bata lokaci ba.”
Duk wata cibiyar hada hadar kudade da ta bijirewa wannan umurni na CBN, to babban bankin ya ce “za a ci tarar ta, tare da hukunci mai tsanani.”
A cewar CBN, “shiga cikin hada hadar crypto currency ko kuma sahalewa masu hada hadar bi ta hannunka don musayar kudade ta tsarin, haramun ne a Nigeria.”
Takardar wacce ke dauke da sa hannun Bello Hassan, Daraktan sa ido na bankin da kuma Musa I Jimoh, daraktan tsarin biyan kudade na babban bankin, ta ce wannan umurnin zai fara aiki nan take.
Takardar ta kuma ce CBN a shekarun baya ya “gargadi bankunan ajiyar kudade (DMBs, cibiyoyin hada hadar kudade da ba bankuna ba (NBFIs) da kuma sauran cibiyoyin hada hadar kudade (OFIs) da daukacin al’umma da su kauracewa yin hada hadar kudaden crypto curreny.