“Da INEC za ta kasance a tsaka tsaki, to da ba za a riƙa rikici a zaɓe ba” – Gwamna Eno
Gwamna Eno yace idan INEC ta kasance a tsaka-tsaki wajen zaɓe, da ba za a yi rikicin zabe ba a Najeriya.
Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya buƙaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da ta kasance a tsakiya yayin gudanar da zabe a kasar.
Eno yayi wannan kiran ne a lokacin da sabon kwamishinan zaɓe na Jihar Mista Isah Ehimeakhe ya kai masa ziyarar ban girma a gidan Gwamnati da ke Uyo a ranar Laraba.
A cewar gwamnan, idan alkalan zaɓen suka kasance tsaka-tsaki, wato ba su goyon bayan kowace Jam’iyya, to da babu bukatar yin tashin hankali a lokacin zabe.
Ya ce “Munyi imanin cewa za ku ci gaba da kasancewa tsaka tsaki a harkokinku kamar yadda aka saba”.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: Emefiele Ya Garzaya Kotu, Yana Neman A Sauya Sharuddan Belin sa
Mu a matsayinmu na al’umma mun yi imanin cewa idan ku ka kasance a tsaka-tsaki, to ba za a yi tashe-tashen hankula ba, ya kamata mu gudanar da zabe domin mu bar Ra’ayin Jama’a ya yi tasiri.
Sannan Kuma mu sani, mu da al’umma suka zaɓa, to za mu zama abin tambaya ga al’umma dangane da abinda muke yi musu, domin kuwa su ne suka kai mu ga wannan matakin.
Gwamnan ya kuma umarci INEC da ta kasance masu kirkire-kirkire wajen bullo da tsare-tsare da za su ci gaba da inganta harkokin zabe a kasar nan.
Gwamnan ya kuma a amince da yadda hukumar zaɓen ta gudanar da sahihin zabe na tsawon lokaci, yana mai bayyana hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben Gwamnan Jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris a matsayin nasara tare da tabbatar da ingancin INEC.
Eno ya taya Shugaban hukumar zaben Jihar murna kan naɗin da aka yi masa, ya kuma buƙace shi da ya ƙara jajircewa wajen tafiyar da hukumar musamman ta ɓangaren kasancewa tsaka-tsaki domin cigaba da kasancewar ta a yadda aka santa.