A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace kadarorin filaye guda 40 na tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu na wucin gadi, wanda a halin yanzu yake tsare a kasar Birtaniya.
Punch ta ruwaito cewa, Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan wani kudiri da Ibrahim Buba ya gabatar a madadin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
A WANI LABARIN KUMA: Tsofaffin Za Su Bar Madafin Iko A Shekarar 2023– Wizkid
Yayin da yake bayar da wannan umarni, Alkalin ya umarci hukumar EFCC da ta wallafa umarnin kwace kadarorin na wucin gadi a kowace Jaridar da ake wallafa kullun rana dake kasar nan cikin kwanaki bakwai masu zuwa.
Ya kuma ba da umarnin cewa duk wanda ke da sha’awar kadarorin da aka kwace ya bayyana kansa a cikin kwanaki 14 bayan fitar da dokar ta wucin gadi.
Sai dai daga bisani, Mai shari’a Ekwo ya dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga Disamban shwkarar 2022 don bayar da rahoto.
Umurnin kwace kaddarorin na wucin gadi ya kunshi kadarorin Ekweremadu kamar haka; Kaddarori 10 a Enugu, uku a Amurka, biyu a Burtaniya, daya a Legas, tara a Dubai, da kuma 15 a babban birnin tarayya Abuja.
A yanzu haka dai tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan da matar sa na gurfana a gaban kotu a kasar Birtaniya kan zargin cire wasu sassan jikin dan Adam, wani lamari kuma da ba ya da alaka da kadarorin da aka ce an kwace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Yuwuwar Kaiwa Amurika Hare-Haren Ta’addanci Kwanan Nan— Birtaniya
Kasar Birtaniya, ta yi gargadin cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hari a Kasar Amurka. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ta kuma shawarci ‘yan kasarta da ke kasar da su yi taka tsantsan tare da kaucewa tarukan jama’a.