Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Litinin a birnin Abu Dhabi, sun kammala wata yarjejeniya mai cike da tarihi, wadda ta yi sanadiyar dakatar da dokar hana shiga kasar ga yan Najeriya nan take.
Bugu da kari kuma, bisa wannan yarjejeniya mai cike da tarihi, kamfanonin jiragen saman Etihad da na Emirates, za su dawo da jadawalin tashi da saukar jiragen sama a Najeriya nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
KARANTA NANGwamnatin Tarayya Ta Karbo Bashin Dala Miliyan 163 Domin Noman Alkama-Shettima
Kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya, wannan dawo da ayyukan jirage nan take, ta hanyar wadannan kamfanonin jiragen sama guda biyu da kuma tsakanin kasashen biyu, bai shafi wani kudi da gwamnatin Najeriya za ta biya nan take ba.
Bisa la’akari da yunkurin bunkasa tattalin arziki na diflomasiyya da kuma shawarwarin da shugaba Tinubu ya gabatar a yau ga takwaransa, an kafa tsarin da aka amince da shi, wanda zai kunshi wasu sabbin jari na biliyoyin daloli na dalar Amurka a cikin tattalin arzikin Najeriya a bangarori da dama, ciki har da tsaro. noma da sauran su, ta hannun jarin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya ji dadin yadda ya samu nasarar yin shawarwarin hadin gwiwa, sabon shirin musayar kudaden waje tsakanin gwamnatocin biyu, wanda za a bayyana dalla-dalla a cikin makonni masu zuwa.
A WANI LABARIN KUMAAmbaliyar Ruwa Tayi Ajalin Mutum 150 A Libya
A karshe, shugaban na fatan yaba wa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, kan abokantakarsa ba tare da bata lokaci ba, da kuma kokarin da ya yi na hada kai da shi, domin daidaitawa da sake dawo da martabarta, matsayin dangantakar dake tsakanin muhimman kasashen biyu.