Yayin da ake cigaba da gwabza kazamin fada a yankin Tigray, dakarun gwamnatin tarayyar Habasha da kawayen su sun shiga garin Shire dake yankin.
BBC ta ruwaito cewa, Wannan dai wata nasara ce tun bayan kaurewar fadar a cikin watan Agusta wanda ya wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta na watanni biyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wike Ya Goyi Bayan Takarar Gwamnan APC, Tare da Juya Baya Ga Dan Takararsu Na PDP
Dakarun yankin Tigrai sun bayyana shigar dakarun gwamnatin a matsayin na wucin gadi kuma sun sha alwashin ci gaba da fafatawa da su.
Garin Shire na daya daga cikin manyan biranen da ke cikin yankin Tigray kuma al’ummar garin sun kai kimanin 100,000.
Har ila yau, ita ce cibiyar gudanarwa na arewa maso yammacin Tigray kuma daya daga cikin birane hudu na yankin dake da filin sauka da tashin jiragen sama.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan yakin da ya barke a watan Nuwamba shekarar 2020, dubun mutane ne suka yi gudun hijira daga wasu sassan yammacin Tigray yayin da wasu da dama ke samun mafaka a makarantu daban daban.
Haka kuma kasa da kilomita 100, wanda yayi daidai da mil 62 daga garin Shire akwai wasu manyan biranen guda biyu wadanda ake kira Axum da Adwa masu matukar tarihi.
Kazalika tare da kwarin guiwa da nasarorin da ta samu, gwamnatin tarayyar Habasha za ta iya zuwa Axum da Adwa, wanda hakan zai ba su damar shiga babban titin da zai kai Mekelle, babban birnin yankin Tigray.
Sai dai kiraye kirayen dakatar da yakin da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi wani abune da dakarun Tigrai suka yi maraba dashi, amma gwamnatin Habasha ta ce za ta kwace filayen jiragen sama da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayyan a yankin na Tigray.
Hakan na nuni da samun kwarin gwiwa bayan kusan watanni biyu ana gwabza fada da kuma nuna cewa tashe tashen hankula na iya ci gaba da barkewa sanadiyar yakin.
Idan za’a iya tunawa a watan Agusta, Firaministan kasar Abiy Ahmed ya yi zargin cewa jiragen da ke dauke da makamai na sauka da daddare a Shire da ake kyautata zaton masu tallafa wa sojojin Tigray ne, amma Mista Abiy bai bayyana daga inda jiragen suka fito ba.
A wata sanarwa da ofishin yada labaran na gwamnatin kasar ya fitar a jiya litinin ya kuma zargi mayakan yan tawayen na Tigrayan da hada kai da wasu yan kasashen waje da ba a bayyana sunayensu ba wajen keta sararin samaniyar Habasha a matsayin hujjar yanke shawarar sarrafa tashoshin jiragen sama.
A WANI LABARIN KUMA: Ko Yanzu Yan Najeriya Sun Gamsu Da Ayyukan Raya Kasa Da Muka Samar – Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu ya bude taron karshe na duba kokarin ma’aikatu karkashin gwamnatinsa inda ya ce an gudanar da ayyukan raya kasa wadanda suka gamsar da ‘yan Najeriya.
Yayin da yake jawabi a taron da aka shirya domin auna irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufofi guda 9 na gwamnatinsa, shugaban kasar ya bayyana irin nasarorin da aka samu a fannin noma da tattalin arziki da ayyukan raya kasa da tsaro da lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.