Dakatar da Bawa: Dalilin da ya sa ba zan iya caccakar Tinubu ba – Omokri
Reno Omokri, mai fafutukar tabbatar da turbar siyasa da zamantakewa, ya ce ba zai iya caccakar Shugaba Bola Tinubu ba sakamakon dakatarwar da ya yi wa Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ba da dadewa ba.
Omokri ya ce ba zai iya kai caccakar Tinubu ba domin a cikin makonni biyu da hawansa mulki, Tinubu ya kawo karshen tsarin tallafin mai, ya dakatar da yajin aikin da a ke yi a fadin kasar, ya kuma kawo karshen yawan canjin kudi.
KARANTA WANNAN LABARIN:NAFDAC ta fasa kamfanin sarrafa maganin Baban Aisha a Kaduna
Babban mai sukar Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Tinubu dai ya dakatar da Shugaban Hukumar EFCC ne har abada don ba da damar gudanar da bincike mai inganci kan zarge-zargen da ake masa.
Sai dai Omokri ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “Tallafin man fetur ya tafi, Bawa na EFCC ya tafi, barazanar yajin aikin NLC ya lalace, canjin kufi ya tafi, layin man fetur ya tafi.
“Kuma kuna so in kai hari ga mutumin da ya samu wannan nasara cikin makonni biyu kacal? Ina ganin sai in fayyace matsayina in tsaya. Ni dan siyasa ne na adawa. Ma’ana ina adawa da jam’iyyar da ke mulki kuma ina yawan fadi idan ta yi kuskure.
“Kuma zan yi duk mai yiwuwa don ganin Waziri Atiku Abubakar ya samu adalcin da yake nema a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
“Duk da haka, ni ba mai neman ballewa ba ne da ke fakewa a karkashin fafutukar siyasa don lalata Najeriya. Ina son Najeriya, kuma ina son ta yi nasara. Kuma a kan haka, ba ni da uzuri.
A wani labarin kuma:Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC Bawa
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura takardar sallamar aiki ga Shugaban Hukumar Kula da ta’annati Mr. Abdulrasheed Bawa daga ofishin sa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda daga Daraktan yada labarai na Shugaban Kasa, Willie Bassey domin gudanar da bincike akan Zarge-zargen da Ake yo masa a lokacin da yana ofis.
Wannan ya biyo bayan Zarge-zarge Mai Karfi da Ake yi masa.