By Abbas Yakubu Yaura
Akalla dalibai 100 ne a makarantun firamare da dama a Ilori ta tsakiya suka ci gajiyar rabon kayan makaranta kyauta a jihar Kwara .
Taron wanda ya gudana a fadin makarantu biyar ya kunshi dalibai 20 a kowace makaranta wanda wata kungiya mai zaman kanta mai suna Gidauniyar Yusuf Zulu Gambari ce ta dauki nauyin gudanar da taron.
Makarantun sun hada da makarantar sakandaren gwamnati ta Oke Aluko, sai makarantar firamaren gwamnati dake karamar hukumar Center Igboro,da makarantar sakandaren gwamnati ta Ojagboro da kuma sakandaren gwamnati ta Okelele.
Da take jawabi a daya daga cikin abubuwan da aka gabatar, shugabar gidauniyar, Alhaja Halimat Zulu Gambari ta ce gidauniyar an yi ta ne da nufin ciyar da marayu da zawarawa da marasa galihu gaba.
Ta ce gidauniyar ta gano cewa da yawa daga cikin daliban ba su da karfi a fannin ilimi sannan ba su da abubuwan da ake bukata.
Sannan ta kara da cewa: “Mun tura ma’aikatanmu zuwa makarantar da kansu suka tantance wadanda suka ci gajiyar shirin. Yanzu mun ba da riga, amma muna fatan za mu ci gaba da biyan kudin makaranta da sauran bukatunsu na ilimi.
Ta shawarci daliban da su kasance masu jajircewa tare da daukar karatunsu da muhimmanci, sannan ta yi alkawarin cewa gidauniyar za ta ci gaba da bayar da shawarwari da samar da yanayi mai kyau don ci gaban karatunsu.
A nasa jawabin, shugaban makarantar United Junior Secondary School, Babatunde Sulyman Dagbo ya godewa gidauniyar bisa wannan karamci da suka yi, sannan ya shawarci daliban da su kasance masu jajircewa da kula da rigunan.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Yesira Ayomide Abdulqodir, dalibar JSS 2, ta godewa gidauniyar bisa wannan karimcin tare da yin kira ga sauran jama’a da su yi koyi da su domin gyara halin da marasa galihu ke ciki a makarantu.
Shima a nasa bangaren, Ibrahim Muhammed, dalibin JSS 3 ya nemi karin taimako kan kayan rubutu da kudin makaranta da dai sauransu.