By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu matafiya da masu ababen hawa suka makale yayin da daliban kwalejin fasaha ta D.S. Adegbenro ICT dake Itori, jihar Ogun suka tare hanyar Legas zuwa Abeokuta, domin nuna adawa da sace wasu abokan aikinsu guda biyu.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa wasu masu satar mutane sun kai hari a dakin kwanan dalibai a Afowowa, cikin karamar hukumar Ewekoro ta jihar Ogun da misalin karfe 1 na safiyar ranar Laraba.
Daliban sun ce sun fusata ne saboda ‘yan sandan sun ki amsa kiran da aka yi musu na nuna damuwa, inda suka ce harin ya dauki kusan sa’o’i hudu ba tare da wani kalubale daga jami’an tsaro ba.
Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “’yan fashin sun kai hari a wani hostel da ke Afowowa kuma sun shafe kusan sa’o’i hudu suna gudanar da aiki.
“Sun tafi da na’urar kwamfutoci da sauran kayan abokan aikinmu. Mun kira ‘yan sanda, amma babu amsa. Daga baya ‘yan sandan sun ce motarsu ba ta da kyau.
“Lokacin da suka isa, sai suka ce daliban su jagoranci ‘yan fashin. An harbi daya daga cikin daliban a kafa, wasu kuma sun samu munanan raunuka. Don haka ne muka bazama kan tituna domin yin zanga-zangar.”
Daliban wadanda tun da farko sun yi tattaki zuwa ofishin ‘yan sanda da ke yankin, sun tare babbar hanyar da ta hada Abeokuta da Sango-Ota da Legas.
Matasan da ke kan hanyar sun yi ta zirga-zirga na tsawon sa’o’i, yayin da matasan suka dage cewa ba za su bude hanyar ba har sai an ceto abokan aikinsu da aka yi awon gaba da su.
An bayyana cewa an jefi wasu motocin ‘yan sanda da duwatsu a farkon gudanar da zanga-zangar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce yana sane da faruwar zanga-zangar.
Sai dai Oyeyemi ya ce ba a yi masa cikakken bayani kan musabbabin faruwar zanga-zangar ba.