Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai na ƙasa Abubakar Bukola Saraki ya bayyana dalilan da yasa ya zama Likita.
Saraki yace ya zama Likita ne domin yabi sahun babanshi Baban sa, tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattijai a jamhuriya ta biyu Sanata Olusola Abubakar Saraki, wanda abokanan sa da masoyan sa suke kira ‘Oloye’.
Dayake jawabi a wani taron Lafiya na ƙasa da ƙasa, da ƙungiyar ɗaliban Likitanci suka shirya (NiMSA), tsohon Gwamnan Jahar Kwara ya tausaya masu da suka zama Likita, inda yace ya zama likita abune na yiwa Al’umma aiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku zaɓarwa Jami’iyyar APC nagartattun shuwagabanni a zaɓe mai zuwa a Jahar Katsina — Saƙon Jikan Hambali ga ƴaƴan Jami’iyyar APC
Yayi nuni dacewar, yayi matuƙar farin ciki daya gansu a matsayin likitoci, musamman daya yi taro dasu a taron Lafiya na ƙasa da ƙasa.
“A gidanmu, zama likita shine abinda zakayi ka cigaba da taimakon mutane masu buƙata, a lokacin da nake da shekaru 12, na gano cewa ina son in zama Likita, sabudda Oloye Mahaifina Likita ne.
“Shekaru da dama da suka gabata, lokacin tana da shekaru 12, ɗaya daga cikin ɗiyata, wadda yanzu tana shekara ta 4 a karatun ta na Likitanci, ta bayyana cewar itama tana son ta zama likita a wata rana.
“Wannan ne ya sanya nake jindaɗi inga likitoci masu hazaƙa, wanda sune shuwagabanni wanda zasu bada kyakkyawar kulawa ta lafiya ga ƴan Najeriya,” ya rubuta a shafin sa na Twitter