Dalilin da ya sa aka zaftare kasafin kudin Mataimakin Gwamnan Edo – Kakakin Majalisa
Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Honarabul Blessing Agbebaku ya yi karin haske kan dalilan da suka sa aka karkatar da kudaden da aka ware wa ofishin Mataimakin Gwamna na kasafin kudin 2024 zuwa kimanin Naira miliyan 345 yayin da na Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Shugaban Ma’aikata (HoS) da sauran su yafi yawa.
Ya kara da cewa ba wani nauyi mai yawa da za a baiwa mataimakin gwamna a sabuwar shekara saboda burinsa na zama gwamna.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kwamishinan Ondo ya yi murabus saboda mutuwar Akeredolu
A lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ci gaban da aka samu a ofishin sa, Agbebaku ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa na cewa akwai rashin jituwa a tsakanin wasu ‘yan majalisar kuma suna shirin hana shi zaman lafiya.
A cewarsa, “Ba kamar sauran ofisoshi kamar SSG, HoS da sauran su ba, ofishin gwamna da mataimakin gwamna daya ne, ba a kasafin kudin bana kadai ba, hatta a shekarun baya haka abin yake.
A wannan karon, gwamnan ya bayyana karara cewa tunda mataimakin gwamnan bai gudanar da ayyukansa ba a shekara mai kamawa, saboda burinsa, wanda ya gane cewa yana da yawa kuma yana daukar lokaci, yawancin ayyukansa sun koma wasu ofisoshi kuma gwamna yana da ikon yin hakan.
“Dukkanmu mun san cewa mataimakin gwamna ba shi da ikon da tsarin mulki ya ba shi sai abin da gwamna ya ba shi.
Don haka galibin abubuwan da mataimakin gwamnan ya saba yi, gwamnan ya cire masa. Har ma ya shiga kafafen yada labarai yana korafin cewa ba ya aiki, idan ba aiki kake yi ba, wa zai ba ka kudi?
“Ba a ba ku kuɗin a matsayin kyauta na sirri ba, ana bayar da su ne don aiki don haka idan ba ku aiki, a zahiri kuɗin ba zai zo ba kuma babu yadda za a yi ku yi aiki yadda ya kamata yayin da kuke ingiza wannan buri.
A wani labarin kuma:Kwamishinan Ondo ya yi murabus saboda mutuwar Akeredolu
Raimi Olayiwola Aminu, kwamishinan ma’aikatar gine-gine, filaye da gidaje na jihar Ondo, ya yi murabus daga mukamin nasa.
Wannan ci gaban na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan an rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar Ondo bayan rasuwar Oluwarotimi Akeredolu.